Facebook zai kawo sabon tsari Najeriya

Hakkin mallakar hoto AP

Hamshakin kamfanin intanet din nan na Facebook ya kaddamar da wani shirin shiga shafin da cin gajiyar wasu abubuwa kyauta ba tare da data ba a Najeriya, kasar da ta fi kowacce yawan al'umma kuma inda facebook din ta fi samun kasuwa a nahiyar Afrika.

Dandalin zai bayar da dama ga masu amfani da shafin su samu shiga shafukan intanet kyauta tare da hadin gwiwar kamfanin sadarwa na Airtel, wanda shima ya mamaye kasar a matsayin na uku cikin kamfanonin sadarwar da suke gaba-gaba, inda yake da mabiya miliyan 34.

Kyautar da aka sanya wa suna Free Basics, na cikin tsarin shafin na Facebook, wanda ke neman bayar da damar samun kashi biyu bisa uku na kasashen duniya, inda kamfanin ke cewa ayyukan da ake gudanarwa ya taimaka wajen shigar da jama'a fiye miliyan 25 duniyar yanar gizo.

A Najeriya kadai akwai mabiya shafin Facebook miliyan 16, kuma tsadar kudin shiga intanet din na janyo cikas ga cigaba da shiga ga masu amfani da wayoyin salula.

Sabon tsarin dai na cike da cece-ku-ce, ya kuma sha suka saboda ba kowane abu mabiyan za su samu damar amfana da shi kyautar ba.

Shugaban Facebook din Mark Zuckerberg, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewar, shafin zai bayar da damar samun labaran duniya da bayanai kan kiwon lafiya, da na neman aiki, ba tare da an biya ko sisi ba.