An samar da wuraren cajin waya a Harami

Babban ofis mai kula da masallacin harami a Makkah ya ƙaddamar da wuraren cajin wayar salula na musamman.

An kuma ƙaddamar da wuraren cajin wayar salula a masallacin Annabi (SAW) dake Madinah.

Jaridar Saudi Gazatte ta ce, cikin watan Oktoba ne aka sanar da shirin samar da wuraren cajin wayar domin bada damar cajin wayar salula ga masu ibada.

An samar da wuraren cajin wayar salulan ne a jikin turaka da dama dake cikin masallacin na Ka'abah.

A kowanne wuri dai akwai wuraren da za a iya cajin wayoyin salula guda 8 a lokaci guda.

Amma kuma a lokuttan da ake da cunkoso a masallatan kowanne mutum zai yi cajin wayar salula na minti 8 ne kawai.