Ko za ka iya zama a birnin Jos na Nigeria?

Hakkin mallakar hoto

Bisa ga dukkan alamu zaman lafiya na Ζ™ara inganta a Jos, babban birnin jihar Pilato da ke Najeriya, bayan zubar da jini da aka kwashe ana zubar da jini a birnin .

Tashin hankali na addini da kabilanci ya yi kamari a birnin da ma jihar ta Filato baki daya.

A baya jama'a daga wasu wurare na fargabar zuwa, ko da su bi su wuce ne.

A yanzu, bisa dukkan alamu, babban birnin na Jihar Filato ya hau turbar zaman lafiya, inda aka kwashe tsawon lokaci babu tashin hankali.

Kasuwanci da sauran harkokin rayuwa na yau da kullum na gudana yadda ya kamata, kamar dai yadda mazauna birnin suka shaidawa wakilinmu Ishaq Khalid a wannan rahoton.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti