Nigeria: Litar man fetur ta koma N145

Hakkin mallakar hoto Getty

Daga yanzu dai 'yan Nigeria zasu rika sayen litar man fetur akan naira 145.

Ranar Laraba karamin ministan man fetur Dokta Ibe Kachikwu ya sanar da hakan.

Sai dai kuma ministan ya ce farashin man ba zai haura 145 kowacce lita ba.

Hukumar PPPRA ce ke da alhakin daidaita farashin man fetur din a Najeriya, kuma ta bayar da bayanin cewa ta dauki wannan matakin ne domin ci gaban al'ummar kasar, da kasuwannin man fetur din, da kuma tattalin arzikin kasar baki daya.

Wata sanarwar da ta fito daga sakataren gudanarwa na hukumar, Sotonye E. Iyoyo, ta ce ana shawartar gidajen mai mallakin kamfanin NNPC a fadin kasar da su sayar da nasu man kasa da N145 ga kowacce lita.

Hukumar ta PPPRA ta kuma ce tana sane da wahalhalun da al'ummar Najeriya ke fama da su a 'yan watannin da suka gabata, kuma domin tunkarar wadannan matsaloli, za ta bi hanyoyin da za a tabbatar da cewa jama'a ba su cutu daga wannan kari da aka yi ba.

A wata sanarwar da ta fito daga ofishin mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo, ta ce a ranar Laraba da yamma ne ya yi wata ganawa da masu ruwa da tsaki a harkar mai.

Taron, a cewar sanarwar, ya samu halartar shugabannin majalisar dokoki da kungiyar gwamnoni da kungiyoyin kwadago na NLC da TUC da NUPENG da kuma PENGASSAN.

Karin bayani