Brazil: Roussef ta ɗauki mataki kan tsigewa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Zanga-zangar nuna kin jinin mulkin Dilma Roussef a Brazil.

Shugabar Brazil, Dilma Rouseff ta bukaci kotun ƙolin kasar ta dakatar da yunƙurin tsigeta.

Wannan dai matakin karshe ne na katse shirin yin kuri'a a majalisar dattawa dangane da batun.

Shugabar ta Brazil dake fama da fadi tashin siyasa, ta musanta zargin da ake yi mata na yin amfani da kasafin kudi lokacin zaɓe.

Idan dai har wasu daga cikin 'yan majalisar dattawan suka jefa kuri'ar amincewa da yunkirin tsige shugabar, to hakan zai bude kofar soma shirin tsige ta, a ranar Laraba.