Dalilin rikicin makiyaya da manoma a Nigeria

Image caption Najeriya na fuskantar rikicin makiyaya da manoma.

Masana na ganin cewa kai zuciya nesa, tare da kokarin gwamnatoci da shugabannin al'umma wajen wanzar da zaman lafiya, ka iya taimakawa wajen shawo kan matsalar rikicin Fulani makiyaya da manoma, a Najeriya.

Rikici tsakanin manoma da Fulani makiyaya dai na ci gaba da zama wata gagarumar matsala, wadda ke barazana ga zaman lafiya da haɗin kan ƙasar.

Rashin fahimta ne ke janyo rikici tsakanin makiyaya da manoman kamar dai yadda wakilinmu AbdusSalam Ibrahim Ahmed ya farga a cikin dajin dake gefen wani gari a jihar Enugu:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti