Ana kada kuri'a kan tsige shugabar Brazil

'Yan majalisar dattawan Brazil sun kwashe awowi 18 suna kada kuri'a a kan ko za a tsige shugabar kasar Dilma Roussef ko a'a.

Ana zargin shugabar kasar ne dai da boye gagarumin gibi a asusun kasar gabanin sake zaben ta a shekarar 2014.

Sai dai ta musanta zargin, yana mai bayyana yunkurin tsige da cewa tamkar juyin mulki ake son yi wa mulkin dimokradyya.

Akasarin 'yan majalisar dai sun ce za su kada kuri'ar tsige Misis Roussef tun ma kafin su shiga zauren majalisar.

Za a dakatar da ita daga mulki da zarar 'yan majalisar sun amince a tsige ta.

Kafin su fara kada kuri'ar dai, sai da Misis Roussef ta bukaci kotun kolin kasar da ta hana su yin kuri'ar.