'Ka dawo ka yaki cin hanci'

Hakkin mallakar hoto AFP

A Ghana, a yayin da shugaba John Mahama, ya ke barin kasar domin zuwa halattar taron kolin kasashen duniya kan yaki da cin hanci a Biritaniya, kungiyoyin fararen hula a dukan fadin kasar sun yi kira gareshi da yayi dauki darasi daga taron domin matsa kaimi wajen yaki da matsalar da ke neman zame wa kasar karfen kafa.

Kungiyoyin farar hular dai sun yi kiran ne a wata sanarwa da suka fitar bayan wani taro da suka gudanar Accra, babban birnin kasar, gabannin bude taron na Biritaniya.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ga wakilin mu Iddi Ali, da karin bayani.