Iran bata daidaita da Saudiyya ba kan Hajji

Kasar Iran ta kasa cimma yarjejeniya tare da mahukuntan Saudiya game da shirye shiryen tura 'yan kasarta aikin hajjin bana a watan Satumba.

Mahukuntan Iran din sun zargi Saudiyya da yin abin da suka kira amfani da dokokin lalata al'amura a yarjejeniyar.

An samu zazzafar takaddama tsakanin giwayen yankin biyu da basa ga muciji bayan aikin hajjin bara, inda sama da Iraniyawa dari 4 suka mutu a turmutstsun da aka yi, wanda ya yi anadin mutuwar mahajjata sama da dubu daya.