Uganda: An rantsar da Yoweri Museveni karo na 5

Image caption Museveni ya yi tazarce karo na biyar

An rantsar da Yoweri Museveni a matsayin shugaban ƙasar Uganda karo na biyar, bayan zaɓukan da aka yi ta taƙaddama akai.

An ɗau tsauraran matakan tsaro a Kampala, babban birnin ƙasar, inda aka rufe hanyoyin sadarwa.

A ranar Laraba ne aka kama babban jagoran 'yan adawa, Kizza Besigye, bayan da ya rantsar da kansa a matsayin shugaban ƙasa a wajen wani biki da ba na hukuma ba.

Ya ce shi ne mutumin da ya lashe zabukan.

A hukuman ce dai Mista Museiveni ya samu sama da kashi sittin cikin ɗari na ƙuri'un da aka kaƙa a zaɓukan da aka yi a watan Fabrairu.

Sai dai 'yan adawa da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil adama da ƙasashen yamma da dama sun ce ba a yi zaɓen cikin gaskiya da adalci ba.