BBC za ta yi aiki tare da kamfanoni a Lagos

Image caption BBC tana son kara yawan masu bibiyarta zuwa miliyan 500 a 2020.

An zabi kamfanoni guda a birnin Legas na Najeriya domin fara aiki da fasahar da suka kirkiro wajen taimakawa BBC ta cimma burinta na kama 'yan Afirka matasa ta kafar Intanet.

Kamfanonin sun haɗa da Codulab da Team Timerail kuma dukkan su suna birnin na Legas.

Wannan dai na daya daga cikin burin BBC na kara yawan masu bibiyar shirye-shiryenta zuwa miliyan 500, a 2020.

A baya dai an gudanar da bayani kan wannan shirin a birnin Nairobi na Kenya da Cape Town na Afirka ta Kudu, a inda kuma aka samu nasarar fara shirin.