Akalla mutane 90 sun mutu a Habasha

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Mutane akalla 90 ne aka tabbatar sun mutu a Ethiopia sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwaryar da aka kwashe kwanaki ana yi wanda ya haddasa ambaliya da zabtarewar kasa a sassan kasar.

Haka kuma wasu mutanen fiye da dubu 400 ne suka rasa matsungunansu, inda hukumomi ke tsoron cewar adadin zai iya karuwa fiye da haka kwarai.

Ethiopia na fuskantar daya daga cikin munanan farin da bata gani ba cikin kusan shekaru 50 da suka gabata, inda mutane kusan miliyan 1.4 a halin yanzu da suka dogara da masu kai daukin abinci.