Mace ta zamo sakatare janar na FIFA

Hakkin mallakar hoto FIFA
Image caption Fatma Samoura ta yi aiki da Majalisar Dinkin Duniya a sashen kula da harkokin bil adama.

Hukumar kwallon kafa ta FIFA, ta bai wa wata mace mai suna Fatma Samoura, mukamin Sakatare Janar.

Wannan shi ne karo na farko da hukumar, wacce maza suka fi mamaya, ta bai wa macce babban mukami irin wannan.

A yanzu, Fatma Samoura, wacce 'yar asalin Senegal ce, tana aiki ne da Majalisar Dinkin Duniya, a matsayin jagorar harkokin bil adama a Najeriya.

Misis Samoura za ta maye gurbin Jerome Valcke, wanda aka kora a watan Junairu, sakamakon zargin sa da hannu a matsalolin cin hanci da rashawa da hukumar ta Fifa ta shiga a bara.

A yayin da ya ke bayyana mukamin na ta, shugaban na FIFA Gianni Infantino, ya ce za ta kawo sabon yanayi ga hukumar, tamkar da wani aka kawo daga waje.