South Africa: Cutar huhu ta kama mahaƙan gwal

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ma'aikatan kamfanonin hakar gwal suna murnar hukuncin da kotu ta yanke

Tsofaffin ma'aikatan da suka yi aiki a kamfanonin haƙar gwal, a Afirka ta Kudu, sun ce sun kamu da cutar huhu sakamakon ayyukan da suka yi.

Ma'aikatan dai sun ce sun kamu da cutar 'silicosis', mai yi wa huhu illa wadda kuma ba ta warkewa.

Hakan ne yasa wata kotu a Johannesburg ta yanke hukunci cewa ma'aikatan za su iya haɗa ƙarfi wajen cigaba da neman haƙƙinsu.

Hukuncin dai zai ba wa ma'aikatan wata dama da ba a taba samu ba a tarihin kasar.