Kenya ta dauki mataki kan kwayoyin kara kuzari

Hakkin mallakar hoto Getty

Hukumomin kasar Kenya za su tura ministocin kasar biyu hedikwatar hukumar hana shan kwayoyi masu sanya kuzari da ke Canada, domin tattaunawa kan matakin da hukumar ta dauka na ayyana kasar da wadda ta take dokokin ta.

Sanarwar na zuwa ne bayan shugaba Uhuru Kenyatta ya kira taron gaggawa da jami'an hukumar wasanni ta kasar.

Ministan wasannin kasar, Hassan Wario ya ce Kenya za ta yi aiki kafada da kafada da hukumar WADA domin samun daidaito game da batun da aka nuna damuwa, gwamnati ta dauki matakan da suka dace domin magance matsalar cikin gaggawa wadanda suka hada da tattaunawa kai tsaye da hukumar WADA.