Mutumin da ya ke taimakawa dalibai satar amsa

Dalibai da dama suna so su mayar da hankali kan karatunsu. Sai dai akwai masu yiwa dalibai rubutu kuma su biya su da dama, wadanda a shirye suke su taimakawa wadanda ba su damu da karatun ba.

Marek Jezek shine sunan bogin da yake amfanin da shi yanzu, amma akwai wasu da dama. Yana da hikima da kwazo kuma yana so ya koyi karatu. Kuma akwai da yawa.

Wadanda suke irin wannan harkar masu kwazo ne sosai wadanda suka kammala karatun digiri da sakamo na ajin farko wato "first-class", kuma akwai dogon jerin sunayen jami'oi inda ake kai ayyukan.

Rubutun "dissertation" na nufin rubutun da daliban jami'a ke yi a kan kwas din da suka karanta, ta yadda za su bayyana fahimtarsu da kwarewarsu a kan karutun da suka yi idan sun kawo karshen karatun.

Amma sai dai idan irinsu Jezek basu yi wa dalibi rubutun ba.

Marubuci ne mai zaman kansa a wani bangare na masana'antu da ke bunkasa sosai. Kamfanoni masu yi wa dalibai rubutu domin a biya su na cigaba da fitowa karara suna bayyanawa dalibai irin bukatarsu.

Hakkin mallakar hoto bb

A watan da ya gabata ne dai wani kamfanin yi wa dalibai rubutu ya lika hoton tallar irin aiki da suke yi. " Kana bukatar ayi maka rubutu?" Tambayar da suka yi kenan, inda suka yi ikirarin cewa dalibai dubu goma sun yaba da irin aikin da suke yi."

Da na tuntu ɓi kamfanin safara na London (TFL) mai kula da jirgin kasa kuma, na yi mai bayani a kan irin aikin da kamfanin tallar yake yi, sai TFL ya ce ba su lura ba amma zasu cire hotunan tallar kuma ba za su sake yarda a lika su ba.

A makon da ya gabata a lokacin da wani kamfani ya ke rarraba katin talla ga dalibai a jami'ar Queen Mary da ke London, suna ikirarin su kwararru ne a yi wa dalibai rubutu kuma suna taimakawa dalibai su samu sakamakon da su ke so".

Wani shafin yanar gizo ya na bai wa dalibai damar wallafa aikin rubuce-rubuce da aka sakasu su yi a makaranta da kuma ranar da suke bukata a shafin, kuma marubutan na yi musu.

Da alamun dai jami'oi na fama wajen gano kan lamarin. Babbar matsalar ita ce kusan da wahala a gane ko wani ne ya yi wa dalibi rubutu.

Kusan duka jami'oi suna amfani da na'urar da ke gano ko mutun ya yi satar amsa wajen yin rubutunshi wanda ake kira Turnitin, wanda ke duba kalaman da aka sata daga wani marubucin daban. Amma na'urar ba za ta yi wani zargi a kan wani mawallafi ya rubuta ba.

Kudin da ake biya na farawa ne daga fan 150 da aikin jami'a kadan zuwa dubban fan, idan za a yiwa dalibi rubutun kawo karshen karatu da ake kira dissertation.

Marek Jezek yana karbar fan 2,500 ga rubutun karshen karatu. Ya ce yana da wani muradi na musamman a kan aikin - ramuwa.

* Wani mataki ne jami'oi za su dauka domin dakile masu yiwa daliabi rubutu a biya su?

Shawarwari da jami'oi suka bayar sun hada da: *Rage dogara da rubutun *A yawaita ganawa da dalibai a kan rubutun da su ke yi *A bukaci dalibai su dinga baiwa malamai rubutun da suke yi a azuzuwansu, da kuma a dinga duba daki-daki na rubutun da suke yi kafin su kammala. *A kara yawan gwaji da baki maimakon rubutu

Kusan duka jami'oin da ke Birtaniya na amfani da na'urar tantance ko an yi santar amsa a rubutu wanda ake kira Turnitin. Sai dai na'urar ba ta yi nasara ba sosai wajen gano sahihanci rubutu.

Yana da digirin digir-gir a wani babban jami'ar Birtaniya kuma ya ce ya nemi aikin koyarwa ko mai bincike sama da 300, amma kuma bai samu ba. Ya yi ammanar wariyar launin fata ne ke janyo rashin samun aikin.

Jezek dan asalin Jamhuriyar dimokaradiyar Congo ne kuma ya yi bayani a kan malaman makaranta wadanda suke da alaka da Afirka da suka kasa samun aiki a jami'oi.

Dakta Adam Longcroft, darakta ne a jami'ar East Anglia da ke haddadiya daular larabawa, ya ce dalibi ba zai iya bogin jarabawar da ake yi ba baki ba kuma yana tare da kalubale da dama. Hankalin dalibai na tashi matuka da irin wannan jarabawar. Mutane da dama na tsoron magana a mutane, amma yana da muhimmanci kowani dalibi ya iya magana a cikin jama'a."

Wani mataki da ganin da aka dauki na ganin an kawo karshen nuna wariya wajen tsarin duba jarabawa yana sawa ya yi wuya dalibai su yi satar amsa.

Jami'oi da dama suna da tsarin aikawa mallaman jami'a aikinsu ba tare da sun saka sunansu ba, ta yadda mallamin jami'a ba zai iya saka dalibi ya fadi jarabawa ba a dalilin kabilanci ba.

Amma idan har mai duba jarrabawar bai san ko wanene ya aika takardar jarabarwar ba, idan dalibi mai tsaka-tsakin fahimta ya aika da rubutu ba za a iya zaton wani almundahana ba.

Shin Jezek yana ganin cewa taimakawa dalibai wajen satar amsa laifi ne?

Ya ce " ina ji ba dadi amma kuma ina ga duka bangarorin biyu ne zasu ji ba dadi, Amma masu yin wannan harkar bamu da yawa. Kuma ina ga jami'oi ma suna da alamar tambaya a kan irin wannan sana'ar tamu."

Ya yi ammanar cewa wasu jami'oi basu yin bincike a kan daliban da suke zargi saboda basu da kwararan hujja, kuma suna tsoron yawaitar hakan zai iya bata sunan jami'oin nasu idan aka gano cewar ana satar amsa.

Sai dai jami'oi sun musanta zargin cewa suna jurewa hanyoyin da dalibai ke bi wajen yin satar amsa kuma sun ce su na daukar abin da muhimmanci sosai. Hukumar tabbatar da kyau ta Quality Assurance Agency, da ke saka ido kan karatun gaba da sakandare, a baya bayan nan na bincike domin gano irin tasirin da kamfanonin rubutu ke yi.

Farfesa Phil Newton da ke aiki a jami'ar Swansea ya ce babban kalubale na shawo kan matsalar ita ce shaida. " Babban kalubalen matsalar shi ne akwai yiwuwar a gano. Kuma idan har zaka yiwa dalibi zargin satar amsa, dole sai kana da kwakkwarar shaidar da zai tabbatar da zargin."