Yanayin kwakwalwa na toshe tunani a lokacin mafarki

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Wani bincike da kwararru suka gudanar ya gano cewa, yanayin barci na hana dabbobi su tuna abubuwan da suka koya a baya.

Bayanai sun tabbatar da cewa, zuwa yanzu dai yanayin barci ya na da alaka ta musamman da kwakwalwa.

A yayin da aka tsayar da aikin wasu jijiyoyin kwakwalwa, to yanayin kwakwalwa zai sauya.

A cikin wani rohoto a jaridar likitoci, bincike ya nuna cewa, dan adam na mafarki ne a lokacin da ya ke barci, to sai dai amsa tambayar ko a lokacin, wata sabuwar kwakwalwa ce ya ke amfani da ita ko kuma a'a ta yi wuyar amsawa.