Likitoci sun yi nasarar tiyatar zuciya a Nijar

Hakkin mallakar hoto AP

A jamhuriyar Niger, wasu ƙwararrun likitoci na kasar da kuma na kasar Tunisiya sun yi nasarar aikin tiyatar zuciya da suka yi wa wata yarinya mai shekaru 14.

Yarinyar dai ta kwashe shekaru 7 ne tana fama da matsalar ciwon zuciya.

Aikin wanda ya dau awoyi 3 shi ne na farko da aka taɓa yi a kasar ta Nijar.

Wanan dai wani ci gaba ne da aka samu a ɓangaren kiwon lafiya a kasar ta Nijar, da ta kasance daya daga cikin kasashen duniya mafiya tallauci.

Koda mai ɗakin shugaban Nijar din, Dr Malika Issoufou wadda ita ma likita ce, da ministan kiwon lafiya Malam Kalla Moutari sun halarci wurin da aka yi wa yarinyar aikin.