Nigeria: Gini ya ruguzo a Abeokuta

Wani ginin bene mai hawa huɗu ya ruguzo a kasuwar Itoku da ke ƙaramar hukumar Abeokuta ta jihar Ogun, a Najeriya, a inda mutum daya cikin mutane 16 da ke aiki ciki ya rasu, sauran kuma suka samu rauni.

Hukumar NEMA ta shaida wa BBC cewa, ta ce ta ceto mutane 16 daga ɓaraguzan ginin, amma har yanzu ana binciko wasu mutanen da ake zaton na makale a kasan ginin, ganin yadda yake matattarar jama'a.

Shaidu sun ce har yanzu ba a kai ga gano hakikanin mutanen da suka mutu ba.

Ginin dai ya fado ne da safiyar ranar Juma'a, a lokacin da 'yan kasuwa suke kokarin bude shaguna.