Za a gina gidajen yari na wucin gadi a Najeriya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Za a gina gidajen yari na wucin gadi saboda cunkoso a Najeriya

Majalisar wakilan Najeriya ta ce ta amince da wasu kudade a kasafin kudin kasar na bana don gina wasu gidajen yari na wucin-gadi a kokarin da ake yi na rage cunkoso a gidajen yarin kasar.

Najeriya dai na fama da matsalar cunkoso a gidajen yari, lamarin da ya sa a kwanakin baya shugaban kasar Muhammadu Buhari ya umurci ma'aikatar cikin gida da ta dauki matakan rage cunkoson.

Honorable Jagaba Adams Jagaba, shi ne shugaban kwamitin kula da harkokin cikin gida na Majalisar wakilan, ya kuma yi wa Yusuf Tijjani karin bayani a kan irin halin da gidajen yarin kasar ke ciki.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti