Brazil: Za a jinkirta bude sabon layin dogo sai a lokacin gasar Olympics

Hakkin mallakar hoto Getty

A birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil, za a jinkirta bude wani sabon layin dogo zuwa lokacin da za a fara gasar wasannin motsa jiki na duniya, kuma ba za a bari sauran jama'a su yi amfanin da jiragen kasan ba sai bayan an kammala gasar.

An dai gina layin dogon ne mai tsawon kilomita 16, kuma jiragensa ne za su yi jigilar jami'an gasar da 'yan kallo da kuma ma'aikatan da aikinsu ya shafi gasar.

Mahukuntan birnin sun ce ana sa ran bude tashar ga sauran jama'a bayan an kammala gasar wasannin motsa jiki na nakasassu na duniya, wanda da za a yi a watan Satumba mai zuwa.