Mutane 8000 sun fice daga garinsu saboda gobara a Spaniya

A kasar Spaniya ko Andalus wata gobara ta kaure a wani juji ko bolar da ake jibge tayoyi a garin Sesena, inda wani bakin hayaki ya turnuke sararin samaniya, lamarin da ya tilasta wa dubban jama'a barin gidajensu.

Tuni dai mutum 8000 suka fice daga garin, yayin da ragowar mutum 1000 ke ci gaba da zama.

Sai dai mahukunta sun bukaci ragowar mutanen ma da su fice daga garin, suna gargadin cewa za su fuskanci matsar rashin lafiya.

Bolar dai ta kai girma filayen kwallon kafa guda goma sha biyar.

Wani ayarin 'yan kwana-kwana ya wuni cur yana kokarin kashe wutar, wadda masu bincike suka ce da gangan aka cinna ta.