MDD ta koka kan alakar Boko Haram da IS

Image caption MDD ta nuna damuwa akan alakar da ke tsakanin kungiyar Boko Haram da kuma ta IS

Kwamitin tsaro ko sulhu na Majalisar dinkin duniya ya nuna damuwa dangane da alakar da ke tsakanin kungiyar boko haram da kungiyar IS.

Cikin wata sanarwa, kwamitin ya ce kungiyar boko haram na ci gaba da yin zagon-kasa ga kokarin wanzar da zaman lafiya a shiyyar Afirka ta yamma, da kuma Afirka ta tsakiya.

A bara ne kungiyar boko haram ta yi mubaya'a ga kungiyar IS, kuma an ba da rahoton cewa kungiyar boko haram din na tura mayakanta kasar Libya don shiga kungiyar IS.

Kwamitin tsaron ya yi maraba da taron da za a yi yau din nan, wanda shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke karbar bakuncinsa inda ake sa ran nazarin kokarin da ake yi wajen murkushe kungiyar boko haram.

Ana kuma sa ran shugabannin kasashen yankin da kuma takwaransu na kasar Faransa, Farancois Hollande za su halarci taron.