"Rwanda na son tumɓuke Nkurunziza"

Hakkin mallakar hoto AP

Wani rahoton kwamitin sulhu na majalisar ɗInkin duniya na sirri ya zargi Rwanda da cigaba da goyon bayan 'yan tawayen Burundi dake yunkurin tumɓuke shugaba Pierre Nkurunziza.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ne ya samo rahoton kuma ya ce, ko a bara Rwanda ta cigaba da tallafawa 'yan tawayen Burundin ta fuskar horo da kuɗi da kuma kayan aiki.

A ranar Juma'a ne dai kwamitin dake kula da sanya takunkumi zai tattauna rahoton.

Sai dai Rwandan ta musanta yin katsalandan a harkopkin kasar Burundi.