Anyi belin Shekarau

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Nigeria EFCC ta bada belin tsohon ministan ilimin kasar kuma tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau bayan shafe kwanaki biyu ta na tsare da shi.

Hukumar ta EFCC dai ta tsare tsohon ministan ne bisa zargin karbar wasu kudade da aka samo ta haramtacciyar hanya, a lokacin zaben shugaban kasa a bara.

Shi dai Malam Ibrahim Shekarau ya musanta cewa ya karbi wani abu a kudin, sai dai ya amince cewa a gidan sa aka raba, amma shi ko wajen rabon bai je ba a cewar sa.

Wani babban jami'i a hukumar ta EFCC ya shedawa BBC cewa suna ci gaba da bincike a kan tsohon ministan, kuma idan hali ya yi za su iya neman sa domin amsa tambayoyi.

Malam Shekarau dai a yanzu haka dan jam'iyyar PDP ne, kuma ya taba yin takarar shugaban Nigeria a karkashin rushasshiyar jam'iyyar ANPP.