Boko Haram barazana ce ga al'umma - Hollande

Shugaban Faransa, Francois Hollande ya ce kungiyar boko haram na barazana ga zaman lafiya a shiyyar Afirka ta yamma da Afirka ta tsakiya, duk kuwa da irin nasarar da sojoji ke samu wajen murkushe mayakan kungiyar.

Ya yi wannan furucin ne a wajen wani taro a Abuja, inda ya kara da cewa an yi nasarar katse-hanzarin kungiyar, tare da tilasta wa mayakanta su ja-da-baya, amma da sauran aiki.

Shi ma Sakataren harkokin wajen Burtaniya, Philip Hammond na da irin wannan ra'ayin inda ya ce abu ne da muka saba gani a ko'ina cewa ba a cin yaki da ta'addanci da zunzurutun karfin soji a fagen fama, dole sai an shawo kan zukatan da suka goyi bayan ta'addancin.

Tun da farko, majalisar dinkin duniya ce ta yi gargadin cewa dangantakar da ke kara karfi tsakanin kungiyar boko haram da IS na yin zagon-kasa ga zaman lafiya a shiyyar Afirka ta yamma da Afirka ta tsakiya.