Masoya biyu sun kashe kansu a India

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan sandan India da jami'an asibiti

'Yan sanda a arewacin India sun ce, alamu sun nuna saurayin nan da wata buduruwa, wadanda aka gano gawarwakinsu a wani daki dake rufe, sun kashe kansu ne.

Saurayin da buduruwar, masu shekaru sha takwas da sha tara, sun mutu ne bayan sun cinna wa kansu wuta.

Rahotanni sun ce mutanen biyu sun yi karatu a makaranta daya, amma iyalansu ba su goyi bayan soyayyar da suke yi ba, saboda daya daga cikinsu Musulmi ne, daya kuma mai bin addinin Hindu.

A cikin makon daya gabata, wasu rahotannin sun ce buduruwar ta shirya yin wani aure da wani saurayin daban.

Mutanen da ke auren mabiya wasu addinai daban da nasu a India suna yawan fuskantar suka da tsangwama a shafukan sadarwa na muhawara.