Mutane 14 sun mutu a harin kunar bakin wake a Iraki

Bagadaza Hakkin mallakar hoto ap
Image caption Masana'antar iskar gas da aka kai wa hari a Taji

Mayakan kungiyar IS sun kai harin kurnar bakin wake a masana'antar iskar gas da ke arewacin Bagadaza.

Maharan sun tada motoci uku da ke makare da bama bamai a dayan daga cikin kofofin shiga cikin masana'antar iskar gas ta gwamnati a garin Taji.

Haka kuma wasu 'yan bindiga da ke sanye da rigar bama bamai sun kutsa kai cikin masana'antar.

Wata majiyar tsaro ta ce mutane akalla 14 aka kashe ya yinda sama da 20 sun ji raunuka.

Ta ce dakarun tsaron kasar sun dakile harin tare da taimakon jiragen sama na yaki na kasar Irakin.

Sai dai rahotani sun ce an cinnawa tankokin iskar gas guda uku wuta.