"Nigeria na cin gajiyar 'yan ci rani"

Wani rahoto da aka fitar a baya baya nan ya nuna cewa Najeriya ita ce ta 6 a jerin kasashen duniya da ke samun kudi daga 'yan kasashensu dake aiki a kasashen waje.

Rahoton ya kuma ce Najeriya ita ce ta farko a kasashen da ke kudu da Sahara inda 'yan kasarta da ke zama a kasashen waje suka aika da sama da dala biliyan 34 a shekarar da ta wuce.

Masana sun kuma ce kudaden na taimakawa wajen rage talauci a kasar.

Dr Huseini Abdou shi ne shugaban kungiyar yaki da talauci ta Plan international da ke Najeriya, kuma a hirarsu da Raliya Zubairu ya yi bayani kan irin tasirin da wannan fanni ya ke yi ga tattalin arzikin kasa ga yadda hirar ta su ta kasance;

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti