Karancin abinci a kasar Mozambique

Mozambique Hakkin mallakar hoto
Image caption Ambaliyar ruwa a kasar Mozambique

Mozambique ta ce ba ta da isashen abinci da za ta rabawa mutane kusan miliyan daya da fari ya shafa a kasar.

Ta ce abincin da take da shi na mutane dari biyar ne kawai.

Mozambique na fuskantar matsalar fari a yankunan da ke kudanci da kuma tsakiyar kasar da kuma ambaliyar ruwa da ruwan sama kamar da bakin kwarya a arewacin kasar.

Mutane akalla arbain ne suka rasu.

Lamuran sun lalata amfanin gona da dama, kuma sun janyo mutuwar dubban shanu.