An yi taron bunkasa al'adun Nigeria da Nijar

A jamhuriyar Nijar, an yi wani taro tsakanin gwamnoni da sarakunan gargajiya daga arewa maso gabashin Nigeria, da kuma takwarorinsu na yakin Diffa don bunkasa al'adun yankunan biyu da kuma karfafa zaman lafiya a yankin tabkin Chadi mai fama da rikicin Boko Haram.

A ranar Lahadi ne dai aka yi wannan taron a garin Maine-Sorwa na jahar Diffa.

Muhammad Shuwa shi ne magatakardan kungiyar sarakunan gargajiya na arewa maso gabashin Nigeria, ya ce an tattauna yadda za a samu hadin kai a tsakanin kasashen biyu ta yadda za a iya tunkarar duk wani kalubale.

Ya kara da cewa an dauki matakai da dama wadanda za a yi amfani da su wajen kare al'ummar yankunan kasashen daga duk wani tashin hankali ko barazana.