'Gwamnatin Najeriya ba ta da kudin biyan tallafin mai'

Ministan mai na Najeriya Hakkin mallakar hoto twitter
Image caption Dr Emmanuel Ibe Kachikwu ministan mai na Najeriya

Majalisar Dokokin Najeriya ta ce rashin kudi shi ne yasa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta janye tallafin da ake bai wa bangaren man fetur .

Shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawa ta Najeriya, Senata Ali Ndume ya ce ministan mai na kasar Dr Emmanuel Ibe Kachikwu ya bayyana masu cewa a halin yanzu gwamnati ba ta da kudin da za ta biya a matsayin tallafi.

Ya ce hakan ya biyo bayan faduwar farashin mai a kasuwanin duniya da kuma bututun man da aka fasa a yankin Niger Delta.

Senata Ali Ndume ya nemi 'yan Najeriya akan su kara hakuri da gwamnatin Buhari.

A jiya ne dai kungiyar kwadago ta NLC da TUC ta debar wa gwamnatin kasar wa'adin kwanaki uku akan ta rage karin da ta yi wa farashin man fetur ko kuma zasu shiga yajin aiki na sa baba ta gani.