'Yan Najeriya sun koka da rashin gudanar da zaben kananan hukumomi

A Nigeria ana cigaba da nuna damuwa dangane da kwan-gaba-kwan-baya da ake yi wajen gudanar da zabukan kananan hukumomi a jihohi da dama na kasar.

Gwamnonin Jihohi ne dai ke da ikon gudanar da zabukan shugabannin kananan hukomomi da kansilolinsu ta hanyar hukumomin zabe na jihohi,amma a jihohin kasar da dama, kantomomi ake nadawa.

Wannan rashin gudanar da zabe dai na janyo cece kuce saboda shugabannin kananan hukumomin da Kansilolinsu su suka fi kusanci da jama'a.

Tun bayan dawowar Najeriya kan tafarkin mulkin dimokradiyya a shekarar 1999,matakin mulkin kananan hukumomi ke shan wahala da rashin tabbas ta fuskar zabe da wa'adin mulki da ma kudaden gudanarwa inda wasu ke zargin gwamnonin jihohin ne ke hana su 'yanci saboda suke da wuka da nama wajen gudanar zaben.