IS ta kai hari kan asibiti a Syria

Hakkin mallakar hoto SYRIA REBELS GATHERING

Rahotanni daga Syria na cewa mayakan IS sun kai hari kan wani asibiti da ke birnin Deir al-Zour a gabashin kasar.

Masu kare hakki bi'adama sun ce an halaka sojojin gwamnatin Syria kusan 20, an kuma sace jami'an asibitin

kusan rabin birnin dai na karkashin ikon kungiyar IS, wadda burinta shi ne ta kwace iko da birnin baki daya.

Mayakan kungiyar dai sun yi kawanya ga gundumomin da ke hannun gwamnati ta tsawon shekara biyu, kuma ana kyautata zaton gundumomin na kunshe da al'umar farar-hula da ta kai mutum dubu 200.