An halaka sabbin 'yan sanda 25 a Yemen

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Irin mutanen da hare-hare ke ritsawa da su a Yemen

Hukumomi a Yemen sun ce akalla sabbin jami'an 'yan sanda 25 ne suka mutu a wani harin kunar bakin wake a birnin Mukalla dake kudancin kasar.

Kungiyar IS ta ce ita ke da alhakin kai harin, wanda ya auku a lokacin da sabbin 'yan sandan suka yi layi a wata shedkwatar 'yan danda.

A cikin watan da ya gabata ne dakarun gwamnatin Yemen din suka kwace birnin Mukalla daga hannun kungiyar Al-Qaeda.