Zabiya ya yi fito na fito da matsafi

Hakkin mallakar hoto smart factory

Stephane Ebongue ya tsere daga Kamaru a dalilin launin fatarsa, wanda kasancewarsa zabiya ya sa ya fuskanci barazana da dama wajen mutanen da ke da tunanin amfani da ɓangarorin jikin zabiya don yin tsafi na kawo arziƙi.

Bayan shekaru da dama ne ya koma ƙAsarsa domin fuskantar wani matsafi, don sanin dalilin amfani da sassan jikin zabiya wajen yin tsibbu.

Stephane Ebongue ya tsaya a takure a bakin wani daji, kan hanyar da za ta kai shi wajen wani matsafi da ke safarar zabiya.

Yana sanye da kwat kuma dauke da ƙaramin akwati, idanunsa sanye da baƙin gilashi a dalilin fama ciwon idanu da aka san zabiya irinsa na da shi, amma kuma sun ɓoye halin ɗimuwar da yake ciki.

Ya ce, "Zuciyata na bugawa da sauri, saboda ban taɓa ziyartar irin wannan waje ba, sai yau da nake fatan samun amsar tambayoyin da na shafe shekaru ina nema.''

Stephane ya ƙara da cewa, "Ina bukatar sanin dalilin da ya yasa ake kashe zabiya, ina zaton zan iya samun amsoshin ta wannan hanyar."

Stephane dai ɗan jarida ne, kuma yana da zurfin tunani da duba abin da ke gabansa na zahiri, bai yadda da tsafi ba, saboda haka yake zullumin zuwa wannan waje.

A ƙasashen nahiyar Afrika kamar su Tanzaniya da Malawi da asalin ƙasar Stephane Kamaru, an yadda da cewa amfani da ɓangarorin jikin zabiya na kawo sa'a.

Hakan kuma yasa zabiyan da ke waɗannan ƙasashe ke fuskantar barazana ga rayukansu.

"Ana amfani da wasu sassan jikin zabiya, kamar zuciya ko gashinsu ko faratansu, domin wai suna da muhimmanci wajen haɗa magungunan tsubbu, misali samun amfani mai yawa wajen noma, ko yin layar zana ko lashe zaɓe ko kuma samun nasara a ƙwallon ƙafa," In ji Stephane.

Ya ƙara da cewa, "Wannan shi ne dalilin da ya sa ake hallaka zabiya."

Stephane ya ce maƙiyansa uku ne a Afrika, da rana da mutanen da ke ƙyamarsa da kuma matsafa.

Wani rahoto da Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar, ya ce ana sayen sassan jikin zabiya daga dala 2000 har zuwa dala 75,000 idan an samu zabiya sukutum.

Stephane na da shekara 15 lokacin da yayansa Maurice, wanda shi ma zabiya ne ya ɓata fiye da shekaru 30 da suka gabata.

"Wata rana ya fita da safe, bai ƙara dawowa ba," in ji Stephane.

Bayan kwanaki kaɗan sai aka samu gawarsa a cikin daji, duk an yanke sassan jikinsa, an kuma ƙwaƙule kayan cikinsa.

Iyayen Stephane dai sun yi ƙoƙarin bashi tarbiyya mai kyau, kuma basu nuna masa wani bambanci tsakaninsa da sauran 'yan uwansa da ba zabiya ba, sai da ya shiga makaranta ne ya gane cewa daban yake cikin al'umma.

"Da farko na yi ta samun matsala a makaranta, amma iyayena da malamaina suka bani ƙwarin gwiwa, ta yadda kullum ni ke zuwa na ɗaya a ajinmu."

Matsalar ita ce, Ebongue na da matsalar ciwon ido da zabiya irinsa ke fama da shi, hakan kuma ta sa a cewarsa, sau da yawa baya iya rubuta jarabawa a makaranta, saboda rubutun ya masa ƙanƙanta.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Saboda matsalar rashin gani, zabiya na fuskantar matsala wajen karatun a allon makaranta.

A dalilin haka ne ya sha alwashin wata rana sai ya gina ɗakin karatu musamman ga masu irin matsalarsa.

Stephane ya karanta aikin jarida, inda cikin ɗalibai 10,000 shi kaɗai ne zabiya, har ta kai ana kwatance da wajen zamansa.

A shekarar 2007 dai Stephane ya yi aure kuma ya fara aikin jarida a Buea da ke Kamaru, inda wani dutse mai aman wuta yake.

Wannan aman wuta da dutsen ke yi ne ya sauya rayuwar Stephane baki ɗaya.

A cewarsa, "An yarda da cewa idan dutsen ya amayo wuta, to wani ubangiji mai suna Epasamoto ne ke fushi, don haka sai da jinin zabiya zai huce."

Lokacin da dutsen ya yi man wuta a shekarar 1999, wutar ta kwararo har Buea, mazaunin Stephane, sai dai ba a samu waɗanda suka raunata ba, saboda a cewar su, an yanka masa wasu zabiya.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mutane na gujewa wuta, bayan dutsen Kamaru ya amayo wuta a shekarar 1999.

A shekarar 2007 ne aka shiga tsoron sake aman wutar dutsen, inda mutane ke ɗaukar matakai iri-iri domin tsayar da shi.

Stephane ya ce hakan kuma tasa yawancin zabiya suka shiga ɓuya. Kazalika, shi ma hakan ta a ya tsere ƙasar waje, ba tare da matarsa da 'ya'yansa ba su fuskanci barazanar ba saboda su ba zabiya bane.

Ya samu wani keftin ɗin jirgin ruwa ɗauke da katakwaye da ya taimaka masa ya gudu ƙasar Italiya, ɓoye cikin kwaroron jirgin har kwanaki 33.

"Na wahala kam, tunda na bar aikina da iyalina da abokaina, na shiga wani yanayi mara daɗi," a cewarsa.

Ya dai samu sa'ida zamansa a Italiya, inda yake iya yin yawonsa ko'ina ba tare da tsangwama ba.

Hakkin mallakar hoto le pavillion blanc
Image caption Wannan gilashin mai kara girman haruffa ke taimaka wa zabiya wajen karatu.

Ba jimawa Stephane ya koyi harshen Italiya, ya kuma samu wajen zama a ƙasar, inda yake koyawa sabbin zuwa harshen, daga nan ya yi wani aboki Fabio Lepore.

Mazan biyu sun ƙulla abota kuma suka soma shirya labaran bidiyo kan Stephane, wanda suka sanya wa suna ''Bulaguron Jolibeau, sunan da aka san Stephane da shi a gida.

Wannan ne kuma dalilin da yasa bayan shekaru biyar, Stephane ya je har Kamaru, da nufin son ganin wani matsafi, amma ya yi ta fafutukar ɓoye razanarsa.

Bayan ya yi kusan minti 20 yana tafiya cikin dajin, hoton bidiyon da ake daukar Stephane da Lepore suka nuno wani fili da wata bukkar da aka rataye kayan wanki daga gefe.

Hakkin mallakar hoto smart factory

Matsafin sai ya fito ya tarbe su, yana yi wa Stephane kallon kura ta samu nama a yayin da suke shan hannu da shi.

Stephane da abokin tafiyarsa Lepore suka bi bayan matsafin cikin bukkarsa, inda ya ke tarbar baƙi, suna kallon kayayyakin tsubbu da ke zube.

Bayan sun gama gaisawa sai Stephane ya miƙa masa 'yar kyautar kwalbar baraza, daga nan kuma ya tambaye shi, "Me yasa zabiya ke da muhimmanci a al'adar ƙasar nan."

Hakkin mallakar hoto smart factory

"Watau baka ma san muhimmancin ka ba?" in ji matsafin, wanda idanunsa duk sun kaɗe. Ya ƙara da cewa, "Zabiya irin ka, tun daga gashin kanka har ƙasusuwanka suna da amfani a ƙasar nan."

Stephane dai ya riƙe kansa, ya cigaba da yi wa matsafin tambayoyi, shi kuma yana ba shi amsa, yana mai cewa a duk sati yana samun masu tambayar haɗin daga wajen masu buƙata daban-daban.

"Kana sane da cewa zabiya da yawa na ɓata saboda hallaka su da ake yi?" Stephane ya tambayi matsafin.

Shi ko ya amsa da cewa, "Mutane na fita neman kuɗi ne, kuma su ke kashe zabiya domin neman abin duniya."

Da Stephane ya tambaye shi ko shin ba ya tsoron 'yan sanda su kama shi? Sai ya kaɗa baki ya ce, ''Su ma ai kuɗi suke buƙata.

Hakkin mallakar hoto smart factory

Daga bisani sai Stephane ya ji bai yarda da wajen ba, sai ya ji ya ƙosa ya bar wajen.

Bayan sun koma gida, yana kallon bidiyon sai ya ji dama ya nuna fusatarsa kan lamarin a fili, ya yi da na sanin tafiya ba tare da ya ƙara turke matsafin da tambayoyi ba.

Maimakon ya samu amsar tambayoyinsa dai, sai Stephane ya gane cewa burin matsafin shi ne kawai ya samu kuɗi.

Hakkin mallakar hoto Le pavillion blanc
Image caption Ebongue ya gina wajen karatu mai suna Le Pavillon Blanc a Douala, inda zabiya ke iya karatu cikin sauki.

A yanzu dai Stephane baya son maganganun camfe-camfe inda yake son ya fuskanci ainihin matsalolin da zabiya ke fama da shi, kamar kiwon lafiya da neman ilimi.