Jami'in gwamnatin Sin mafi girma ya isa Hong Kong

Hakkin mallakar hoto
Image caption Dejiang dai shi ne jami'in gwamnatin Sin mafi girma da ya ziyarci yankin tun bayan zanga-zangar kare demokuradiyya da aka yi.

An tsaurara tsaro a yankin Hong Kong sakamakon ziyarar kwana uku da ya fara a yankin.

Zhang Dejiang dai shi ne jami'in gwamnatin Sin mafi girma da ya ziyarci yankin tun bayan zanga-zangar kare demokuradiyya da aka yi.

An girke 'yan sanda 6000, an kuma like dukkan duwatsun kawa na gini da wadanda ke bakin hanya da gam don hana masu zanga-zanga amfani da su wajen jifa.

An kuma kakkafa wasu shingaye masu tsawon mita biyu.

Kungiyoyin da ke rajin kare demokuradiyya dai sun yi alwashin yin zanga-zangar kyamar ziyarar Zhang Dejiang, har ma wasu daga ciki sun yi shirin yin maci daga tsakiyar birnin zuwa gidan gwamnati, inda ake sa ran za a yi masa liyafar karramawa.

Da isar Mr Zhang yankin, ya yi alkawarin cewa zai saurari jama'a tare da yi musu jawabi