Biliyoyin mutane na fuskantar barazanar ambaliyar ruwa

Hakkin mallakar hoto China Central Television

Wani rahoto da kungiyar bayar da agaji ta Biritaniya ta fitar ya yi gargadin cewa biliyoyin mutanen duniya za su fuskanci barazanar ambaliyar ruwa a shekarar 2060, sakamakon matsalolin sauyin yanayi.

Wani bincike da kungiyar ta Christian Aid ta yi, ya ce Amurka da China da Indiya na cikin kasashen da suka fi fuskantar barazanar.

Kungiyar ta kara da cewa birane irin su Kolkata da Mumbai da ke Indiya sun fi fuskantar matsalar.

Biranen da suka fi kowanne shiga ha'ula'i kuma sun fi yawa a nahiyar Asiya, daga su kuma sai birnin Miami da ke Amurka.

Rahoton ya bukaci gwamnati da ta dauki mataki wajen rage hayaki mai gurbata muhalli, ta kuma mayar da hankali ga shirye-shiryen da za su kawar da bala'in da sauyin yanayi ke janyowa.