Iran: An kama masu 'wulaƙanta' ɗabi'un Musulunci

Hakkin mallakar hoto
Image caption Wajibi ne ga mata a Iran su lullube kansu

Hukumomi a Iran sun kama wasu mutane takwas da suke aiki a kamfanonin tallata kayan ƙawa na intanet, da ake ganin aikinsu bai yi daidai da tsarin Musulunci ba.

Wannan kame na cikin wani aikin shekara biyu da ake yi, inda aka gano masu tallata kayan ƙawa suna sanya hotuna a shafin Instagram da sauran shafukan sada zumunta, da ke nuna mata ba ɗankwali ko hijabi.

A wata hira da gidan talbijin, alƙalin kotun da ke yaƙi da msu damfara ta intanet ya zargi kamfanonin tallata kayan ƙawa da yaɗa ɗabi'un da ba su dace da tsarin Musulunci ba.

Ya ce haƙƙin ɓangaren shari'a ne su ɗauki mataki a kan duk wanda aka kama da aikata irin waɗannan laifuka.

Tun a shekarar 1979 bayan juyin juya halin da aka yi a Iran ne ƙasar ta wajabta wa mata sanya hijabi da rufe gashinsu.