Mabarata sun yi zanga-zanga a Kaduna

A ranar Litinin ne wasu mabarata suka gudanar da zanga-zanga a Kaduna da ke arewacin Nigeria, domin nuna taƙaici a bisa dokar hana bara wacce gwamnan jihar ya sanyawa hannu.

Mabaratan dai na cewa gwamnati ta hana bara ne ba tare da samar musu wani abin yi ba.

Mabaratan sun killace hanyar da ke shiga gidan gwamnatin jihar, har sai da aka zanta da shugabanninsu.

Dokar hana bara na cikin sabbin dokokin da ke haifar da ce-ce ku-ce a jihar Kaduna.

Karin bayani