Niger: Lauyoyi sun ƙaurace wa zaman kotu

Lauyoyi a Jamhuriyyar Nijar sun ƙaurace wa zaman kotun ɗaukaka ƙara a Yamai ranar Litinin, bayan kotun ta fara zamanta na shekara-shekara.

Lauyoyin dai suna zargin gwamnatin ƙasar ne da karya wasu alƙawura da ta ɗaukar musu.

Sai dai shugaban kotun ɗaukaka ƙarar ya ce wannan mataki da lauyoyin suka ɗauka zai yi illa ga aikin kotun.

Ana sa ran kotun ɗaukaka ƙarar za ta saurari ƙararraki 35, cikin kwanaki 14 yayin soma zaman nata.

Ga rahoton wakilinmu Baro Arzika kan wannan batu:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti