Tanzania ta kori ma'aikatan bogi 10,000

Hakkin mallakar hoto Statehouse Tanzania
Image caption John Magufuli ya sha alwashin yaki da cin hanci da rashawa.

Gwamnatin Tanzania ta ce ta gano ma'aikatan bogi fiye da 10,000 kuma ta kore su daga aiki.

Ofishin Fiarai Ministan kasar ya ce gwamnati na yin asarar fiye da Dala miliyan biyu a duk wata a kan ma'aikatan bogi.

Hukumomi a kasar sun ce suna ci gaba da tantance ma'aikata domin korar karin ma'aikatan na bogi.

Shugaban kasar ta Tanzania, John Magufuli - wanda aka zaba a watan Oktoba - na yin yaki da cin hanci da rashawa.