WHO ta fitar da ƙa'idojin kaciya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dubban mata ake yi wa kaciya a kasashe daban-daban na duniya

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta fitar da wasu ƙa'idoji a karon farko kan yadda ƙwararru a harkar lafiya za su dinga bayar da magani ga marasa lafiyar da aka yi wa kaciyar mata.

An ƙiyasta cewa kusan mata dubu 250 aka yi wa irin wannan kaciya, waɗanda mafi yawansu a Afrika suke.

Ƙa'idojin sun nuna cewa yawaitar ƙaurar da ake samu a duniya ta sa al'amarin na cin karo da ƙalubale saboda likitocin ƙasashen yammacin duniya ba su da isasshen horo na shawo kan matsalar.

Yawancin marasa lafiyar na fuskantar matsaloli daban-daban, da suka haɗa da zubar da jini da rashin jin daɗin saduwar aure da lokutan haihuwa da kuma yadda hakan ke shafar ƙwaƙwalarsu.