Kun san illar hawan jini?

Ranar 17 ga watan Mayun ko wacce shekara rana ce da aka ware don wayar da kan al'umma game da larurar hawan-jini.

Kungiyar World Hypertension League mai fafutukar hana yaduwar larurar hawan jini ce dai ta assasa Ranar Hawan Jini ta Duniya da nufin wayar da kan al'umma ta yadda za su kauce wa kamuwa da cutar ko kuma yadda za su kula da kansu idan suna da ita.

Lawan Yahaya, wanda aka fi sani da L.Y. yana dauke da wannan larura, kuma albarkacin wannan rana, ya yi wa wakilinmu da ke Kano, Yusuf Ibrahim Yakasai, bayani a kan yadda rayuwarsa take.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Su ma likitoci sun bayyana irin illar da wannan cuta ke yi da kuma hanyoyin da za a bi domin yin riga-kafin kamuwa da ita, da ma hanyoyin magance ta ga wadanda ke fama da ita, kamar yadda za ku ji a hirar da Ibrahim Isa ya yi da

Dokta Salihu Ibrahim Kwaifa:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti