Bill & Melinda ta ware miliyoyi ga mata

Gidauniyar Bill and Melinda Gates ta bayar da sanarwar cewa zata saki dala miliyan 80,000 domin ganin an tsuke ratar da ke tsakanin maza da mata wajen ci gaba a duniya.

Wannan sabon shiri zai taimaka wajen kawo daidaito tsakanin maza da mata, kazalika zai tallafa wa shirin wanzar da ci gaba mai dorewa na Majalisar Dinkin Duniya.

A wani jawabin da daya daga cikin shugabannin gidauniyar Melinda Gates din ta gabatar, a lokacin da ta bayar da sanarwar, ta ce ba gidauniyar Bill and Melinda Gates ne kadai zata bayar da gudummuwar ba, amma har da gwamnatocin wasu kasashe da kungiyoyin agaji masu zaman kansu, wadanda duk suka shiga wata yarjejeniya game da tsarin wanzar da tallafin.

Wannan tsari dai zai duba girma da yanayin matsalolin tattalin arziki, da kuma abubuwan dake sanadiyar gazawar samun gudummuwar mata wajen ci gaba.

Za a kuma duba sahihan alkaluma da zasu kirga mata a duniya, da kuma hanyoyin da za a tabbatar da cewa an san da zaman su, ta yadda gwamnatocin za su dauki alhakin ci gaban su.