Iraq: Bam ya tashi a Baghdad

Hakkin mallakar hoto AP

Masu kai agajin gaggawa sun ce bama-bamai uku da suka tashi a Bagadaza, babban birnin Iraki, sun yi sanadin mutuwar mutum 53.

Ana zargin wata mace 'yar kunar bakin wake da kai harin a wata kasuwa da ke arewacin Shaab, yankin da yawancin mazaunansa musulmi ne mabiya Shi'a.

Sauran bama-baman sun tashi ne a wata kasuwa da ke makwabtaka da yankin 'yan Shi'a da ke kudu da birnin Sadr.

Kungiyar da ke ikirari da kafa daular musulinci, IS ce ta dauki alhakin kai harin.