An karrama dan Nigeria a Indiya

An karrama Ado Abdulkadir, wani dan Najeriyar da ya shiga gasar rawa da waka da harshen Kannada a Indiya.

Ado ya samu wannan karrama ce a bikin rufe gasar a ranar Litinin, inda ya zo na bakwai, bayan da ya doke mutane 10,800 'yan asalin kasar.

Sakamakon haka Ado ya ce, kamfanonin shirya fina-finai uku ne suka yi masa tayin shirin fim sakamakon wannan nasara da kuma fice da yayi a kasar.

Ado dai asalin dan Najeriya ne da yake karatu a jihar Karnataka da ke kudancin Indiya, kuma ya shiga gasar rawa da wakar ne da ake kira 'Re Ga Ma Pa' da harshen Kannada mai wuyar koyo.

Karin bayani