Littafin da ya lashe gasar Man Booker

Hakkin mallakar hoto Getty

Wani littafi da wata 'ya ƙasar Korea ta kudu ta rubuta ya lashe lambar yabo ta Man Booker International ta bana.

Wannan lambar yabo ta marubuta ana bayar da ita kowacce shekara ga litattafin da aka rubuta da harshen Turanci, ko aka fassara zuwa Turanci.

Littafin da ya lashe lambar yabon bana shi ne 'The Vegetarian' wanda 'yar Korea ta Kudu, Han Kang ta rubuta, kuma Deborah Smith ta fassara shi zuwa Turanci.

Da marubuciyar da mai fassara zasu raba kyautar £50,000.

Litttafin, wanda ɗan ƙarami ne ya ƙunshi labari ne akan wata da ta ƙauracewa cin duk wani abu dangin nama, domin nuna rashin amincewa da mummunar halayyar ɗan Adam a hulɗarsa da sauran halittu.

Manufar wannan lambar yabo ita ce, ƙarfafa samar da fassarar Turanci ta labarai da aka rubuta da wasu harsuna.