Rabuwar kawuna kan yajin aiki a Nigeria

Image caption Babbar Sakatariyar gwamnatin Najeriya babu kowa.

An samu rabuwar kawuna tsakanin ƙungiyar ƙwadago ta Nigeria game da yajin aikin da ake yi domin bijirewa ƙarin farashin fetur.

Wani bangare na ƙungiyar ƙwadago, wanda Aliyu Wabba ke jagoranta, ya fara gudanar da yajin aiki, amma bangaren Joe Ajaero ya ce ba zai je yajin aiki na ranar Laraba ba.

Tattaunawa tsakanin gwamnatin tarayya da 'yan ƙungiyar ƙwadagon ta tashi ba tare da samun daidaito ba.

Tuni dai gwamnati ta ce matsayin NLC na shiga yajin aiki duk da umarnin kotu abin takaici ne.

Image caption Gidajen mai da kasuwanni sun bude.

Sanarwar da ke ɗauke da sa hannun sakataren gwamnatin tarayya, Injiniya Babachir David Lawal ta umarci ma'aikata su yi watsi da yajin aikin.

Gwamnati a sanarwar ta ƙara da cewa, duk ma'aikacin da ya shiga yajin aiki to ba za a biya shi albashin ranakun yajin ba.

Wakilin BBC Nasidi Adamu Yahaya, da ya ziyarci babban ofishin gwamnatin tarayya da ke Abuja, ya lura cewa ma'aikata ba su fito ba.

Sai dai kasuwannin birnin da gidajen man fetur da wasu ofisoshin 'yan kasuwa masu zaman kan su suna ta hada-hada.