NASS: An yi watsi da dokar kafofin sadarwa

Image caption Lokacin da 'yan Najeriya suka yi ta zanga-zangar kin kudirin.

Rahotanni daga Najeriya na cewa Majalisar dattawan kasar ta yi watsi da kudirin da ke neman takawa kafafen sada zumunta birki.

Hakan ya biyo bayan rahoton da kwamitin majalisar kan 'yancin dan adam da shari'a ya mikawa zauren.

Rahoton kwamitin dai ya nuna cewa kudirin ya saba ka'ida musamman ta fannin dakile fadin albarkacin baki sannan kuma zai taimaka wajen karuwar matsalar cin hanci.

Daman dai tun farkon gabatar da kudirin a zauren majalisar, 'yan Najeriya suka yi wa majalisar ca, bisa zargin cewa hakan wani yunkuri ne na son dakilewa 'yan kasar fadin alabarkacin bakinsu.

Da ace kudirin ya zama doka, ta da duk wanda aka kama da laifin yi wa wani kage ko sharri,to da zai fuskanci hukuncin zaman gidan kaso na shekara biyu.